IQNA

An Cafke Wani Malamin Kirista Mai Tsatsauran Ra’ayi A Kenya

22:16 - October 09, 2017
Lambar Labari: 3481984
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Kenya sun damke wani malamin addinin kirista mai tsatsauran ra’ayi da ke tunzura mabiyansa zuwa ga tashin hankali.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Pol Makanizi malamin addinin kirista ne na darikar Angalican, kuma yana dauke da akidu na tsatsauran ra’ayi da nuna kyama ga sauran addinai.

Daga cikin abubuwan da yake aikatawa kuwa har da samar da wasu dalibai 53 da yake koyar da su irin akidarsa da tunaninsa, inda suke daukar tunanin tayar da fitina da kin sauran addinai.

Mahukuntan kasar Kenya sun jima suna bin diddigin abin da yake aikatawa, amma daga karshe dai sun yanke shawarar kame shi domin nisantar da shi daga bainar jama’a, da kuma binciken lamarinsa domin ya fuskanci hukunci daidai dokar kasa.

3650251


captcha