IQNA

An Girmama Wanda Ya Kafa Cibiyar Ibn Sina A Wurin Mauludin Manzon Allah A Masar

23:52 - November 30, 2017
Lambar Labari: 3482153
Bangaren kasa da kasa, an girmama wani masani dan kasar Masar da kaa cibiyar ilimi ta ibn Sina a wurin taron mauludin manzon Allah (SAW) a Masar tare da halartar shugaban kasar.
An Girmama Wanda Ya Kafa Cibiyar Ibn Sina A Wurin Mauludin Manzon Allah A MasarKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar yanar gizo ta yaum sabi cewa, an bude wannan taron jiya a a bababn dakin taruka na birnin Akahira tare da halatar shugaban kasar Masar Abdulfattaha Sisi.

Baya ga shugaban na Masar Ahmad Tayyib shugaban cibiyar Azahar, Muhamma Mukhtar ministan kula da harkokin addini na kasar Masar, Shauki Allam bababn maia bayar da fatawa a kasar, duk sun halarci wurin.

Haka nan kuma wasu daga cikin manyan fitattun malaman kasar da suka hada da limaman juma’a na wasu manyan masallatai a branan kasar duk sun halarci wurin.

A karshen zaman taron na jiya bayan sauraren karatun kur’ani da kuma bayanai kan matsayin da daraja da wadannan ranaku na tunawa da haihuwar manzon Allah suke ad shi da muhimmancin raya su, an girmama Muhamamd Bushara, shugaban kwamitin ayyuka na musulmia nahiyar turai, uma shugaban kwamitin muuslmin kasar Faransa, kuma shugaban cibiyar ilimi ta bn Sina.

3668162


captcha