IQNA

Abdulmalik Alhuthi:

Idan Saudiyya Ta Ci Gaba Da Kai Hari Da Killace Yemen Za Su Kai Hari Kan muhimman Wurare A Saudiyya

23:51 - December 01, 2017
Lambar Labari: 3482156
Bangaren kasa da kasa, jagoran kungiyar ansarullah ya bayyana cewa idan masarautar Saudiyya ta ci gaba da kai hari da kuma killace al’ummar Yemen suma za su ci gaba da ai hari kan muhimamn wurare mallakin masarautar Saudiyya.
Idan Saudiyya Ta Ci Gaba Da Kai Hari Da Killace Yemen Za Su Kai Hari Kan muhimman Wurare A Saudiyya

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Abdulmalik Al-Houthi ya bayyana cewar al'ummar Yemen ba za su taba mika wuya ga Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila ba, kamar yadda kuma ya ja kunnen gwamnatin Saudiyya dangane da ci gaba da killace kasar Yemen din da take yi.

Abdulmalik al-Houthi, shugaban kungiyar Ansarullah din da aka fi sani da 'yan Houthi na kasar Yemen ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen bikin Maulidin Manzon Allah (s) da aka gudanar a kasar ta Yemen inda ya ce duk da irin matsalolin da al'ummar kasar Yemen suke ciki sakamakon ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da ake yi a kansu, amma dai suna da karfin gwiwa da kuma tsayin dakan da ba za su taba mika kai ga Amurka da Haramtacciyar kasar Isra'ila ba.

Yayin da ya koma kan irin wuce gona da irin da Saudiyya take yi wa al'ummar Yemen din musamman ma ci gaba da rufe dukkanin hanyoyin kai agaji ga al'ummar Yemen din ta kasa da ruwa da sama, Abdulmalik al-Houthi ya ja kunnen gwamnatin Saudiyyan da cewa lalle al'ummar Yemen suna da hanyoyin magance wannan matsalar kuma lalle idan bukata ta taso za su yi amfani da wadannan hanyoyin.

Har ila yau kuma shugaban kungiyar Ansarullah din yayi kakkausar suka ga akidar wahabiyanci da ya ke ganin yin maulidin Annabi a matsayin wata bidi'a amma a daidai lokacin da mahukutan Saudiyyan kuma suke girmama shugabannin Amurka musamman shugaban Amurkan na yanzu.

3668454


captcha