Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, a jiya ne aka fara gudanar da gasar kur'ani mai tsarki karo na tara da ake yi wa take da gasar Khartum a hukumance kasar Sudan tare da halartar makaranta da mahardata 71 daga kasashen duniya.
Muhammad Rasul Takbiri shi ne yake wakiltar jamhuriyar musulunci ta Iran a wannan gasar, inda a daren jiya ya amsa tambayoyin da aka yi masa na share fagen shiga gasar gadan-gadan.
Daga cikin surorin da ya amsa tamabya akansu akwai Al Imran, Hud da kuma Mujadalah.
Wannan gasa ana gudanar da ita a babban dakin taruka na birnin Khartum kamar yadda aka saba gudanarwa.