IQNA

Taron Tunawa Da Kisan Musulmi A Quebec

22:15 - January 24, 2018
Lambar Labari: 3482331
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da zaman taro na tunawa da musulmin da aka kashe a masallacin garin Quebec na kasar Canada a shekarar da ta gabata a unguwar (St. Catharines).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kungiyar yaki da ayyukan ta'aaddanci na Niagara  zata shirin gudanar da zaman taro na unawa da musulmin da aka kashe a masallacin garin Quebec a shekarar da ta gabata.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro dai zai kunshi mutane daban-daban da suka hada da musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, domin nuna goyon bayansu ga zaman lafiya.

A daren 29 ga watan Janairun shekarar da ta gabata ce dai wani dan ta'adda ya bude wutar bindiga a kan musulmi a lokacin da suke gudanar da salar ishai a wannan masallaci, inda wasu daga cikinsu suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata.

Al'ummar kasar Canada da dama daga cikinsu basu kallon musulmi a matsayin hatsari, yayin da wasu masu kyamar musulunci wadanda su ne kalilan, suke ta hankoron tunzura sauran mutane a kan musulmi.

Gwamnatin kasar dai ta bayyana abin da ya faru kan msuulmia  lokacin da cewa aiki ne na dabbanci, kuma ba zata maince da cin zarafin musulmi ko nuna musu kyama ba, kuma duk wanda ya yi hakan zai fuskanci shari'a.

3685030

 

 

captcha