IQNA

Taro Mai Taken Gudunmawar Juyin Muslunci A Iran A Kasar Ghana

23:07 - January 27, 2018
Lambar Labari: 3482339
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman taro mai taken juyin juya halin muslucni da gudunmawarsa wajen ci gaba a duniya a kasar Ghana.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wannan mako ne za a fara gudanar da taron kwanaki goma na cin nasarar juyin juya halin musulunci a Iran wanda zai gudana a kasar Ghana.

Wannan taro dai yana daga cikin tarukan da aka saba gudanarwa a duk lokacin zagayowar lokutan tunawa da samun nasarar juyin juya halin muslunci a Iran, kamar yadda kuma akan gudanar da irinsa a wasu ofisoshin jakadancin Iran a wasu kasashe.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan taro zai gudana ne a karamin ofishin jakadancin Iran da ke kasar ta Ghana, tare da halartar shugaban karamin ofishin jakadancin da wasu jami'an diplomasiyyar kasar.

Haka nan kum aza  agabatar da jawabai kan matsayin juyin juya halin muslunci na Iran wajen wayar da kan al'ummomin duniya domin sanin hakkokinsu da kuma fita daga kangin bautar manyan kasashe.

Daga karshe kuma za a gudanar da baje kolin kayyayakin da ake samarwa a Iran na gargajiya, da suka hada da sana'oin hannu da suka shahara a kasar tarihi.

3685587

 

 

captcha