IQNA

Musulmin Za Su Gudanar Da Shirinsu na Bude Masallatai Ga wadanda Ba Musulmi Ba

23:10 - January 27, 2018
Lambar Labari: 3482340
Bangaren kasa da kasa, masallatai kimanin 200 suka sanar da aniyarsu cewa a ranar 18 ga watan Fabrairu za su gudanar da shirinsu na bude kofofin masallatai ga wadanda ba musulmi ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gzio na Birminham Mail cewa, a kowace shekara masallatai kimanin 500 ne a fadin kasar Birtaniya ke bude kofofinsu ga wadanda ba musulmi ba domin su shiga.

Wannan shiri ana gudanar da shi ne tare da bayar da dama ga mutane masu son su san yadda musulmi suke gudanar da ayyukan ibada a cikin masallatai, kuma a amsa musu tambayoyin da suke da su a kan addinin muslunci.

Mutane da dama ne daga sassa daban-daban na kasar Birtaniya suke karba kiran musulmi, inda suke halartar masallatai da cibiyoyin musulmi domin ganin yadda musulmi suke gudanar da lamurrnsu na ibada.

Babbar manufar hakan dai ita ce kawar da mummunan tunanin da wasu suke da shi a kan musulmi da addinin muslunci, ta yadda ganin yadda musulmi suke da kuma join  ta bakinsu dangane da addininsu, zai taimaka wajen rage wannn matsala.

3685625

 

captcha