IQNA

Morocco Ce Kasar Da Tafi Kashe Kudade Wajen Gina Masallatai A Faransa

22:40 - February 13, 2018
Lambar Labari: 3482391
Bangaren kasa da kasa, majalisar dattiajan Faransa ta ce kasar Morocco kasar da tafi kashe kudade wajen gina masallatai a kasar ta Faransa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Morocco World News cewa, daga shekarun 2011 zuwa 2016, Morocco ta kasha fiye da euro miliyan shida wajen aikin  ginin masallatai a kasar Faransa.

Tun a cikin shekara ta 1905 kasar Faransa aka kafa dokar hana gina wuraren ibada a kasar.

Saudiyya ce take biye ma Morocco wajen kasha kudi domin gina masallatai a faransa inda ta kasha euro miliyan 3.8 a cikin wannan lokaci, yayin da kuma Aljeriya take  amatsayi na uku da euro miliya 2.

Wadannan kudade da kasashen waje suke kashewa musamman Morocco, Saudiyya, Aljeriya, Kuwait, Qatar, UAE da kuam Turkiya wajen gina masallatai a Faransa, na matsayin kashe 20 cikin dari ne na dukkanin kudade da ake kashewa wajen gina masallatai.

Saboda haka adadin masallatan da suke Faransa ba su wuce 2450 ba, kuma kashi 64 daga cikin masallatan fadinsu murabbai bai wuce 150 ba.

Yanzu haka dai mabiya addinin muslunci su ne a mataki na biyu wajen yawa a kasar Faransa bayan kiristoci.

Emanuel Macron shugaban kasar Faransa, ya bayyana cewa a cikin 2018 yana da nufin saka mabiya addinai daban-daban a cikin dukkanin harkokin tafiyarwa na kasar.

3691155

 

captcha