IQNA

Mutane 391 Suka Shiga Gasar Kur’ani Ta UAE

23:52 - April 09, 2018
Lambar Labari: 3482553
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki da sunnar manzo a kasar hadaddiyar daular larabawa a garin Sharjah tare da halartar mahardata 391.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na lomazoma.com cewa, a jiya ne aka fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki da sunnar manzo a kasar hadaddiyar daular larabawa a garin Sharjah tare da halartar mahardata 391a mataki na kasa da kasa.

Wannan dais hi ne karo na hud da ae gdanar da wannan gasa, amma shi ne karo na farko da ake gudanar da ita a matai na kasa da kasa, inda dliban jami’a ne suke gudana da gasar, 370 ‘yan kasar ta hadaddiyar daula larabawa ne daga jami’oi 26 na kasar, yayin 21 kuma jami’oi daga wajen kasar.

Rashad Salim shi ne shugaban jami’ar Qasimiyya da ke garin Sharjah ya bayyana cewa, wannan gasa tana daga cikin gasar kur’ani mafi muhimmanci da ake gudanarwa a kasar, inda kuma yanzu ta koma ta kasa da kasa.

Ana gudanar da gasar a bangaren hardar dukkanin kur’ani, sai kuma a bangaen hardar juzui 20, sai kuma 10 da kuma 5.

3704141

 

 

 

 

captcha