IQNA

Sayyid Nasrullah: Ranar uds Rana Ce Ta Nuna Damuwa Dangane Da Lamarin Palastine

23:52 - June 08, 2018
Lambar Labari: 3482738
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana ranar Quds ta duniya a matsayin ranar nuna damuwa dangane da halin da al’umma palastin suke ciki.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Nashrah ya habarta cewa, Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana ranar Quds ta duniya a matsayin ranar nuna damuwa dangane da halin da al’ummar palastine suke ciki, da kuma wurare masu tsarki na musulmi da irista, musamman masalacin Quds mai alfarma.

Ya ce babbar manufar ayyana wannan rana ta juma’ar karshen watan Ramadan da Imam Khomeini (RA) ya yi a matsayin ranar quds, ita ce raya lamarin al’ummar palastine da masallacin da sauran wurare mas tsarki da ke karkashin mamayar yahudawan sahyuniya.

Haka nan kuma raya wannan rana da aka yi a birane fiye da 900 a kasar Iran a yau da kuma a kasashen Iraki, Bahrain Yemen da kuma saura mafi yawan kasashen duniya, ya kara tabbatar da cewa lamarin Palastinu ya sake dawowa a raye a cikin zukatan al’umma.

Sayyid Nasrulah ya ce babbar maufar yarjejeniyar nan da ae kira yarjejeniyar karni wadda aka cimmawa tsakanin Saudiyya da Isra’ila da kuma wasu saraunan larabawa ‘yan amshin shata na Amurka, manufar ita ce manatar da al’umma batun Palastinu baki daya.

Daga karshe Sayyid Nasrullah ya ce wadanda suke gwagwamaya a birnin Quds domin kae daraja da martaba ta wannan masallaci mai afarma, alkiblar musulmi ta farko, abin da suke yi suna wakilar dukkanin musulmin duniya ne.

3721071

 

 

 

captcha