Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A cikin bayanin da kungiyar kasashen musulmin ta fitar ta bayyana cewa, gudanar da wannan gasa na a matsayin babban cin zarafi mafi girma ne ga dukkanin musulmi biliyan 1.6 da suke rayuwa a duniya.
Dan majalisar dokokin kasar Holland Geert Wilders mai tsananin kiyayya da addinin mulunci shi ne ya shirya gasar ta zane-zanen batunci a kan manzon Allah (SAW).
Kungiyar kasashen musulmin ta bukaci gwamnatin kasar Holland da ta hana gudanar da wannan gasa, domin hakan baya daga cikin hakkin bayyana raayi ko fadar albarkacin baki ta hanyar yin batunci ga addini ko akidar wasu.