Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau Asabar 15 ga watan Satumban 2018, cibiyar Imam Ali (AS) ta shirya gudanar da babban gangami da jerin gwano a birnin Vienna fadar mulkin kasar Austria domin tunawa da shahadar Imam Hussain (AS) a cikin wannan wata.
A yayin gangamin an yi ta rera taken adalci ga musulmi da kuma kin jinin ayyukan wuce gona da iri da ta’addanci da ake dangantawa da musulmi.
Haka nan kuma an gabatar da jawabaia wurin gangamin, dangane da rayuwar Imam Hussain (AS) da kuma iyalan gidan manzon Allah (SAW) da rin darussan da za a iya koyo daga rayuwarsu mai albarka.
A kowace shekara wannan cibiya tana daukar nauyin shirya tarukan Tasu’a da Ashura inda muuslmi mazauna birnin Vienna sukan halarta, kamar yadda baki daga kasashe daban da suka hada da Iran, Iraki, Turkiya, Afghanista Pakistan da dai sauransu duk suna halarta.