Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron na Saudiyya sun kame mutumin ne bayan da ya yi amfani da bindiga a cikin harabar masallacin annabi (SAW) a daren jiya Asabar, inda ya firgita jama'a da suke a wurin.
Rahoton ya ce babu wanda ya rasa ransa ko samun raunuka sakamakon hakan, kuma yanzu haka yana tsare a ofishin bincike na rundunar 'yan sanda da ke birnin Madina.
Wasu daga cikin wadanda suka sheda abin da ya faru sun bayyana cewa, mutumin wanda babu wanda ya san shi a wurin, ga dukkanin alamu yana fama da matsalar tabuwar hankali.