Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa , shafin yada labarai na Alkhaleej ya habarta cewa, a jiya ne aka bude babban baje kolin littafai a birnin Jidda na kasar Saudiyya tare da halartar cibiyoyi da madaba’antu na buga littafai daga sassa na kasar.
A wannan baje kolin littafai an nuna wani kur’ani wanda shi ne mafi karanta a duniya, wanda tsawonsa ya kai 20mm, fadinsa kuma 15mm, sai kuma tudunsa ya kai 8mm.
Abdulllah Bin Hassan Alkinani shi ne shugaban bangaren kula da harkokin al’adu a kasar Saudiyya, ya bayyana cewa wannan baje kolin yana da matukar muhimmanci, domin kuwa shi ne irinsa na farko mafi girma da aka taba gudanarwa a kasar.
Ya ci gaba da cewa, duk da cewa an dauki shekaru hudu ana gudanar da irin wannan baje koli, amma a shekarar bana an samu ci gaba da fuskar yawan littfan da aka kawo nauoi daban-daban wadanda adadinsu ya kai littafi dubu 180.
Haka nan kuma dangane da yadda mutane suka karbi baje kolin, inda a kowace rana daga ranar da aka fara, a kan samu mutane fiye da dubu 50 da suke halartar wurin.