IQNA

23:23 - January 05, 2019
Lambar Labari: 3483287
Bangaren kasa da kasa, ana shirin bude wata bababr majami'a ta mabiya addinin kirista mafi girma a yankin gabas ta tsakiya da gabashin nahiyar Afrika baki daya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Bawwaba Fito cewa, a yau za a bude bababr majami'a ta mabiya addinin kirista mafi girma  ayankin gabas ta tsakiya da gabashin nahiyar Afrika mai suna Milad Masih a kasar Masar.

Wannan majami'a ita ce mafi girma a yankin, kuma shugaban kasar Masar Abdulfattah Sisi da jagoran mabiya addinin kirista na kasar za su jagoranci bude majami'ar.

An gina majami'ar ne a sabon yankin da ka gina domin ayyukan gwamnati a tsakanin birnin Alkahira da kuma mashiga Swis, inda a nan kuma aka gina babban masallacin kasar, inda za a hada masallaci da majami mafi girma  ayanki guda domin hada kan mabiya addinain muslucni da kiristanci.

A cikin ginin akwai bangaren da aa ware domin Paparoma, kuma wuri da zai iya daukar mutane 8200 masu ibada.

3778348

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، mutane ، Masar ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: