IQNA

Gwamnatin Sudan Za Ta Gyara Tsarin karatun Allo A Kasar

23:21 - March 05, 2019
Lambar Labari: 3483427
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Sudan ta sanar da cewa tana da shirin gudanar da wasu sabbin tsare-tsae dangane da makarantun allo a  kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na gulf365.co ya bayar da rahoton cewa, mataimakin shugaban kasar Sudan Muhammad Yusuf Kibr ya bayana cewa, suna da shirin gudanar da wasu sabbin tsare-tsae dangane da makarantun allo a fadin kasar baki daya, wanda za a fara aiwatarwa nan ba da jimawa ba.

Ya ci gaba da cewa irin wadannan makarantu wadanda aka gada tsawon daruruwan shekaru suna da gagarumin tasiria  cikin al’umma, domin kuwa duk da irin suye-sauye na zamani da aka samu a bangaren karatu a dukkanin bangarori na book da na addini, amma duk da hakan makarantun allo suna da gagarumin tasiri, a kan haka ya ce za su ci gaba da kara inganta tsarin wadannan makarantua  kasar.

Shu ma a nasa bangaren babban daraktan ma’aikatar kula da harkokin addini a Sudan ya bayyana cewa, yanzu haka akwai makarantun alo guda 2,883 wadanda ake daukar nauyinsu a dukkanin jahohin kasar.

3795043

 

 

captcha