IQNA

23:59 - June 20, 2019
Lambar Labari: 3483757
Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron kasar pain sun samu nasarar cafke gungun wasu 'yan ta'adda na kasar Syria a cikin kasarsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya jami'an tsaron kasar pain sun samu nasarar cafke gungun wasu 'yan ta'adda da suke da alaka da 'yan ta'adan Syria  a kasar ta Spain.

Kimanin jami'an tsaron kasar Spain 350 ne suka gudanar da farmakin tare da taimakon 'yan sanda kungiyar tarayyar turai.

An bincika manyan gine-gine guda 14 bayan samun labarin kai komon wadannan mutane, inda aka samu nasarar cafke su.

Daga cikin ayyukansu har da tatatra kudade ta hanoyin da ba halas ba domin aikewa da su zuwa ga 'yan ta'adda a kasar Syria da suke kisan jama'a da sunan jihadi a kasar.

Dukkanin 'yan ta'adda masu dauke da akidar takfir wadanda suke da alaka da kungiyoyin 'yan salafiyya na larabawan da suke zaune a cikin kasashen turai, wadanda ske wanke kwakwalen matasa tare da sanya su hanyar ta'addanci da sunan addini.

3820727

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، spain ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: