IQNA

23:44 - July 10, 2019
Lambar Labari: 3483824
Shugaban majalisar dokokin Lebanon Nabih Birri ya bayyana takunkumin da Amurka ta kakaba wa wasu daga cikin ‘yan majalisar Lebanon na Hizbullah da cewa tozarta al’ummar Lebanon ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jaridar Yni Shafaq ta bayar da rahoton cewa, shugaban majalisar dokokin Lebanon nabih Birri ya bayyana cewa, tozarci ne da wulakaci ga dukkanin al’ummar Lebanon, Amurka ta dorawa ‘yan majlaisar dokokin kasar takunkumi.

Ya ci gaba da cewa wannan mataki ne na siyasar Amurka wanda baya mutunta duk wani tsaro da kaida ta diflomasiyyar kasa da kasa.

Amurka ta kakaba takunkumi a kan wasu daga cikin fitattun kusoshin kungiyar Hizbullah ta Lebanon, da suka hada da ‘yan majalisa biyu, kamar yadda ta haramta wasu bankunan kasar, saboda abin ta kira alakarsu da kungiyar ta Hizbullah.

 

 

 

 

3826173

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: