IQNA

UN: Yanayin ‘Yan Gudun Hijirar Rohingya Bai Dace Da Komawa Myanmar Ba

23:50 - July 24, 2019
Lambar Labari: 3483876
Babbar jami’ar majalisar duniya kan rikicin Myanmar ta bayyana cewa; yanayin da ‘yan kabilar Rohingya suke ciki bai dace da komawarsu Myanmar ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, babbar jami’ar majalisar duniya kan rikicin Myanmar Christine Schraner Burgener ta fadi jiya cewa, bisa la’akari da yanayin da yankunan ‘yan kabilar Rohingya suke ciki a halin yanzu bai dace su koma kasarsu ba.

Ta ce matsalolin biyu ne, yanayin da suke ciki a kasar Bangaladash ba mai kyau ba ne, yayin da kuma a kasarsu Myanmar babu wani tanadi da aka yi domin su a halin yanzu ko da sun koma kasar.

Haka nan kuma ta yi ishara da wajabcin samar da yanayi na kayutata rayuwarsu a  sansanonin da aka tsugunnar da su a halin yanzu, kafin tunanin mataki na gaba, musamamn ma batun mayar da su kasarsu ta Mayanmar.

Tuna  cikin shekara ta 2017 ce dai sojojin Myanmar da kuma ‘yan addinin Buda masu tsatsauran ra’ayi, suka yi kisan gilla a kan dubban musulmi ‘yan kabilar Rohingya a cikin yankin Rakhin, lamarin da ya tilasta kimanin mutane dubu 750 daga cikinsu yin gudun hijira zuwa kasar Bangaladash da ke makwabtaka da kasar.

3829637

 

 

 

 

 

captcha