IQNA

Daruruwan Mutane Sun Musulunta A Kasar Ghana

23:54 - July 24, 2019
Lambar Labari: 3483877
Bangaren kasa da kasa, kimanin mutane 500 sun muslunta a wani kauyea cikin kasar Ghana.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a wani shiri an yada addinin muslucni da wata cibiya take aiwatarwa a Afrika, mutane 473 ne suka muslunta  a kauyen Yabala da ke gabashin kasar Ghana.

Bayanin ya ce a kauyen akwai mutane 1200, kuma kimanin 320 daga cikinsu musulmi ne, a halin yanzu kuma 473 daga cikinsu sun kara musulunta.

Cibiyar yada addinin muslunci ta tausi’at Risala tana gudanar da ayyukanta a kasashe daban-dabana  musamman a yammacin nahiyar Afrika, inda ta kan musuluntar da mutane da dama.

Daga cikin ayyukan da kungiyar take gudanarwa baya ga yin kira zuwa ga addinin muslunci, kuma tana da ayyuka na jin kai da taimakon jama’a, musamman marassa galihu daga cikinsu.

Kamar yadda kuma kungiyar tana gina rijiyoyin burtsatse, da makarantu da kuma asibitoci, kuma ta kan samar da ababe da zasu taimaka ma mutane a bngarorin rayuwarsu, domin kwadaitar da su zuwa ga addinin muslunci.

 

3829706

 

 

captcha