IQNA

Shiri Kan Aikin Hajji A Radiyo Afrika

23:52 - July 25, 2019
1
Lambar Labari: 3483878
Bangaren kasa da kasa, an gabatar da wani shiri a tashar radiyo ta Sautin Afrika kan aikin hajji a birnin Kampala na kasar Uganda.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne Muhammad Reza Qazlasfi ya gabatar da wani shiri a tashar radiyo ta Sautin Afrika kan aikin hajji a birnin Kampala na kasar Uganda dangane yadda ake gudanar aikin da kuma manufofinsa.

A cikin shirin Ustaz Adam wani masani kan harkokin addini a kasa, ya shiga cikin shirin, inda ya gabatar da nasa bayanin.

Dukkanin utanen biyu dai sun yi ishara da cewa, a matakin farko dai aikin hajji ana gudanar da shi ne a matsayin farali a cikin addinin muslunci, baya ga haka kuma yana tattare abubuwa da suka shafi al’ummar musulmi, na hadin kai da yin magana da kalma guda da kuma bayyana izzar musulmi.

Baya ga haka kuma, aikin hajji yana tatatre da yanayi na tarbiyantar da ruhi da kuma kaskantar da kai ga Allah madaukakin sarki, ta hanyr gabatr da wasu abubuwa da suke damfare da wanann aiki babban aiki na ibada.

 

3829924

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
DAGA AKIBU MUAHAMMAD
0
0
ASLM INA YIWA DUKKANIN MAHAJJATAN DA SUKA SAMI DAMAR AIKIN HAJJI DA FATAN ALLAH YASA AYI SHI KARBABBE AMIN.
captcha