IQNA

Wani Malami a Najeriya:

Tozarta abubuwa masu tsarki barazana ce ga zaman tare a cikin al'umma

15:30 - July 09, 2023
Lambar Labari: 3489444
Abuja (IQNA) Wani malami  a Najeriya ya ce: ayyukan batanci irin na kur'ani mai tsarki a kasar Sweden rashin wayewa ne da kuma lalata zaman lafiya da zaman tare a tsakanin al'ummomi.

Malam Yaqub Abdu Ningi daya daga cikin jami’an Mu’assasa Al-Taqreeb da ke Jihar Bauchi a Najeriya ya aike da sakon bidiyo ga IQNA inda ya ce: Mu a wannan gidauniya ta Musulunci muna yin kakkausar suka ga cin mutunci da tsokana na kona Al-Qur’ani da wani mutum ya yi wanda an yi shi ne bayan amincewar hukumomin Sweden.

Ya kara da cewa: Muna kuma yin Allah wadai da kotun da ta ba da lasisin cin mutuncin ra'ayin miliyoyin musulmi tare da cutar da su da sunan 'yancin fadin albarkacin baki.

Abdu Ningi ya ci gaba da cewa: Shin abin yarda ne a ce duk wani mutum daga kowane addini, mai hujja iri daya a mahangar wannan kotu, a ce an ba shi damar cin mutuncin wani da keta dokar da gwamnatin Sweden ta kafa, ko cin mutuncin tutar kasar ta, ko wani abu daban? a zagi wani mai kima a kasar nan da sunan adalci ko fadin albarkacin bakinsa? Hakika wannan aiki ne na wayewa kuma yana lalata zaman lafiya da zaman tare a tsakanin al’umma; Ko dai a kasar Sweden kanta ko kuma a wasu kasashen duniya da musulmi da wadanda ba musulmi ba suke rayuwa kafada da kafada.

Wannan malami na Najeriya ya ci gaba da cewa: “Irin wadannan ayyukan wauta ba su taba rage kimar wannan littafi mai tsarki, kuma wannan aikin yana gamsar da shaidan da ke ingiza masu yin hakan.

Ya yi jawabi ga masu adawa da Al-Qur'ani ya ce: Al-Qur'ani ya kasance maganar Allah, kuma ku da wadanda ke tare da ku, an hukunta ku zuwa ga halaka ta har abada. Duk musulmin duniya za su ba da amsa da ya dace game da wannan wauta da kuka aikata kuma bayan haka, azabar Ubangiji tana jiranku.

4153371

 

captcha