IQNA

Mata Masu Motsa Jiki Da Kuma Hardar Kur'ani A Masar

23:52 - January 21, 2017
Lambar Labari: 3481156
Bangaren kasa da kasa, wasu mata da suke gudanar da wasanni na motsa jiki a wani wuri da ya kebanci mata kawai sun samu damar hardace kur'ani.

BKamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na veto cewa, wurin wasanni motsa jiki na mata da ke garin Aswan a jahar Aswan ta kasar Masar, na gudanar da wasu shirye-shirye na kur'ani mai tsarki

Bayanin ya ce baya ga motsa jiki, matan da suke halartar wanann wuri ana koya msuu karatu da hardar kur'ani mai tsarki, wanda kuma a cikin wani kan kanin lokaci, an samu wasu daga cikin matan da suka hardace kur'ani mai tsarki baki daya.

Aiman Abdulmun'in Mukhtar daya daga cikin jami'an gwamnatin masar ya bayyana cewa, suna jinjiwa wannan wuri da kuma masu tafiyar da shi, ta yadda 'yan mata suka samu damar yin wasanni na motsa jiki,a lokaci guda kuma ana koyar da kur'ani, har ma wasun su sun hardace kur'ani baki daya, a cewarsa wannan babban abin alfahari ne.

Haka nan kum aya yi kira ga sauran mata musulmi na kasar da su yi koyi da wadannan yara mata, kamar yadda kirayi masu wuraren mota jiki da su koyi da wannan wuri.

3564805











captcha