IQNA

Musulmi Yin Gangamin Yin Allawadai Da Harin London

23:46 - March 26, 2017
Lambar Labari: 3481348
Bangaren kasa da kasa, musulmi sun gudanar da wani gangamia garin Birmingham na kasar Birtaniya domin yin Allawadain da harin ta’addancin da aka kai a birnin London.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, daririwa mabiya addibnin muslunci ne suka gudanar da jerin gwano da gangamia birnin Birmingham na kasar Birtaniya domin nuna takaicinsu kana bin da ya faru na harin ta’addanci a London.

Waqqar Azmi wanda shi ne ya jagoranci wannan gangami ya bayyana cewa, tun kafin wannan lokacin ‘yan ta’adda sun kasance suna barazana ga dukkanin bil adama, kuma abin da ya zama wajibi kowa ya sani shi ne ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi abin da suke yi ba shi da wata alaka da addinin muslnci.

Ya kara da cewa, wadannan mutane da suke dauke da akidar wahabiyanci da kafirta sauran musulmi, suna kai hare-hare a kan musulmi tare da yi musu kisan gillafiye da yadda suke yi a kan sauran mabiya addinai, inda ya buga misali da kisan gillar da suke yi wa musulmia kullum rana a kasashen Siriya da kuma Iraki.

Daga karshe masu gangamin sun yi shiru na tsawon minti guda domin nuna alhininsu ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon wannan hari da aka kai a birnin London a cikin wannan mako.

3585707

captcha