IQNA

An Dawo Da Wani Dadadden Kur’ani A Kasar Masar

23:35 - January 07, 2019
Lambar Labari: 3483294
Bangaren kasa da kasa, an dawo da wani dadadden kwafin kur’ani zuwa kasar Masar bayan sanya shi a  kasuwa a birnin London.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Cairo 24 ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar yada al’adu ta kasar Masar ta dawo da wani dadadden kwafin kur’ani zuwa kasar ta Masar bayan sanya shi a  kasuwa a birnin London da nufin fansar da shi.

Wannan kwafin kur’ani dai asalibnsa mallakin Qansu Alguri ne, wanda shi ne sarkin Masar kafin zuwan Daular Usmaniya, kuma an ajiye shi a cikin dakin littafan tarihi na kasar Masar a shekara ta 1884.

An rubuta kur’anin da hannu kuma an yi amfani da fasahar rubutu ta lokacion, duk kuwa da cewa an dauki tsawon shekaru daruruwa da rubuta wannan kur’ani amma har yanzu rubutunsa bai bace ba.

Masu binciken ababen tarihi sun ce bisa ga bincikensu sun gane cewa an rubuta wannan kur’ani tun kimanin shekaru 500 da suka gata ne.

Wani mutum a kasar Birtaniya ne ya mallaki kur’ani, kuma sanya shi a kasuwa wanda za a sayar da shi a ranar 24 ga watan Oktoban 2018, amma gwamnatin Masar ta bukacia  dakatar da cinikin, inda daga bisani ta karbi kur’ani, ba tare da bayyana yarjejeniyar da aka cimmawa kan hakan ba.

3779131

 

 

 

captcha