Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Lemag cewa sarkin Morocco Muhammad na 6 ya hana limaman masallatai a kasar gudanar da duk wani abu da ya shafi siyasa a kasar tare da kiransu da su takaita kawai ga lamurra da suka danganci addini kadai.
A wani rahoton kuma mutanen kasar da dama ne suka gudanar da zanga zanga a birnin Rabat a yau lahadi inda suke Allawadai da tsarin tattalin razikin Priministan kasar wanda har yanzun bai tsinana kome wajen samar da aikin yi ga dimbin matasan kasar ba.
Kamfanin dillancin labaran Nasim ya nakalto shafin yanar gizo na kasar ta Morocco yana fadar cewa mutane kimani dubu guda ne suka fito jerin gwano a birnin na Rabar suna daga alluna dauke da rubuce rubuce kan lalacewar harkokin tattalin arzikin kasar.
A makon da ya gabata ma, dubban ma’aikata daga bangarori daban daban na kasar ne suka gudanar da zanga zanga makamancin wannan a birnin Casablanca duk dai dangane da rashin aikin yi, tsuke bakin aljihu wanda gwamnatin kasar take yi da kuma rashin cika alkawarin samarwa matasa aiki yi wanda gwamnatin tayi a shekarar da ta gabata.
Sarkin kasar ta Morocco Mohammad na 6 dai yana kokarin kwantar da hankalin mutane inda ya yi alkawarin samar da gyare-gyare a tsarin tattalin arzikin kasar da kuma kawo karshen cin hanci da rashwa.
1425822