iqna

IQNA

Dangane da mu
 

 

Dangane Da Mu

Kamfanin Dillancin Labaran Kur’ani Na Kasa Da Kasa (IQNA) A Takaice

Shi ne kamfanin dillancin labaran harkokin da suka danganci kur'ani na farko kuma mafi girma a duniyar musulmi da ke a kasar Iran, wanda aka fi sani a takaice da IQNA, an bude shi a ranar 20 ga watan Aban na hijira shamsiyya 1382, wanda ya yi daidai da ranar 15 ga watan Ramadan na hijira kamariyya 1424, tare da halartar shugaban kasa na lokacin.

Bangare na biyu:

Wannan kamfanin dillancin labarai ya fara ne da labarai 7 a kowace rana cikin Farisanci, bayan shudewar shekaru 19 ya kai yana fitar da labarai 850 a cikin harsuna 21 a kowace rana, inda yanzu yana da labarai na kur'ani fiye da miliyan 1 da dubu 300.

 

Bisa la’akari da yawan yaruka da kuma sakon da wannan kafar yada labaran da suka shafi kur’ani take dauke da shi a matsayi na kasa da kasa, a cikin watan Isfand shekara ta 1391, tare da amincewar bangaren yada labarai da buge-buge na ma’aikatar kula da harkokin al’adun muslunci, an canja sunan wannan kafar yada labarai zuwa kafanin dillancin labaran kur’ani na kasa da kasa, domin kur’ani mai tsarki ya zama hanyar haduwar dukkanin musulmi na duniya.

Manufofi:

- Watsa labaran da suka danganci harkokin kur'ani na cikin kasa da kuma na kasa da kasa

- Kokarin ganin ganin kur’ani ya yi tasiri a cikin Iran da sauran duniya

- Samar da rayayyen tunani a dukkanin bangarori da za su dogara da koyarwar kur'ani

- Samar da rayayyen tunani a dukkanin bangarori da za su dogara da koyarwar kur'ani

- Bayyana tasirin kur'ani a jamhuriyar musulunci ta Iran ga sauran kasashen musulmi

 

 

 

Harsunan IQNA:

Kamfanin dillancin labaran IQNA a halin yanzu yana samar da labarai na kur'ani a cikin harsuna 21, su ne: Farsi, Larabci, Turanci, Faransanci, Urdu, Italiya, China, Rasha, Spain, Istanbuli, Bangala, Hausa, Pashtu, India, Turki, Sawahili, Azari, Indonesia, Philippines, Jamus , Malayo, Portuguese. Kuma yana watsa labaransa ne a shafukan yanar gizo na wadannan harsuna.


 

Rassan IQNA:

Saboda kara tasirin ayyukan kamfanin dillancin labaran IQNA, a cikin tsawon shekaru an bude rassa na cikin gida da waje da suka hada da na larduna, an bude rassa a larduna 30 na cikin kasa, da kuma rassa 6 a sassa na duniya.

1 - Rassan IQNA na larduna su ne:

Ilam, Azarbaijan Gharbi, Azarbaijan Shargi, Ardabil, Alborz, Isfahan, Bushehr, Sistan va Boluchestan, Chehar Mahal va Bakhteyari, Kohzestan, Khorasan Razavi, Semnan, Qazvin, Lorestan, Zanjan, Qom, Khorasan Jonubi, Kerman, Kordestan, Kahgiluyeh va Buyir Ahmad, Golestan, Khorasan Shemali, Kermanshah, Gilan, Fars, Mazandaran, Markazi, Hormozgan, Hamedan, Yazd.

2 – Yankunan Yada Labaran:

Yankin yammacin Asia

Yankin gabashin Asia

Yankin Asia ta Tsakiya

Yankin Turai

Yankin Afrika

Yankin Amurka


 

Ayyaukan labarai:

Sakon kamfanin dilalncin labaran Iqna shi ne, yada koyarwar kur’ani a bangarori daban-daban na adabi, siyasa, fasaha, zamantakewa, tattalin arziki da sauransu……ne, bangarorin labarai na Iqna suna yin iyakacin kokarin domin ganin sun ji ra’ayoyin masu bin su domin fahimtarsu lamurra da suka shafi kur’ani.

Samar da labaran Iqna ya kasu kasha biyu:

A : Bangare na farko ya shafi labarai daga bangarori daban-daban kan batutuwa na yankuna.

B : Bagare na biyu kuwa ya shafi lamurran da suke da dangantaka da kur’ani, da kuma masu bin labaran Iqna gami da muhimman lamurra da suka shafi siyasar wannan kafa.

Haka nan kuma kamfanin dillancin labaran Iqna yana mayar da hankali wajen shawarta malamai da masana wajen fayyace ayyukansa, tare da yin tattaunawa masharhanta da kuma kwararru, daga haka ne yake harhada labaran da yake samarwa.

Iqna a halin yanzu an bangarorin aikin labarai 8 da kuma kanan bangarori 65 kamar haka:

1 – Ayyukan da suka shafi kur’ani (Ayyukan kur’ani ya hada cibiyoyin kur’ani, da kuma fitattun mutane a wannan bangare, da kuma manema labarai)

2 – Siyasa da tattalin arziki (na siyasa da kuma tattalin arziki)

3 – Masaniya (Ilmomi, bangaren Jami’a)

4 –Zamantakewa (Jama’a, lafiya, da kuma yanar gizo)

5 – Adabi da fasaha (adabi, fasaha, rubanya himma)

6 – Na kasa da kasa (Farisanci, Larabci, Ingilishi, Faransanci, Rashanci, Urdu, da sauran yaruka)

7 – Rassan larduna

8 – Wasu kafofi da kuma hotuna

Ayyukan manema labarai na kamfanin dillancin labaran kur’ani na kasa da kasa (Iqna) a shekara ta 83 ne aka fara ayyuka a bangaren manema labarai da kuma aikewa da su domin samar da labarai a kowace rana a mataki na kasa.Wannan gungu a halin yanzu yana da manema labarai 7268 masu rijista, yayin da fiye da 5300 a cikinsu suke aiki, kuma suna iko da rahotanni akalla 120 a kowace rana.

Kamfanin dilalncin labaran (Iqna) baya ga abubwa da kuma manufofin da aka ambata a sama, yana da wasu ayyuka na daban da yake gudanarwa, kamar haka:

A – Gudanar da tarukan kwararru:

B – Fitar da Nashra ta Rayihe:

C – Gudanarwa da halartar tarukan kur’ani: