IQNA - An gudanar da bikin rufe gasar kur'ani mai tsarki ta watan Ramadan a fadin kasar Uganda tare da goyon bayan ofishin kula da harkokin al'adu na Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da hadin gwiwar gidan talabijin na UBC na kasar Uganda.
IQNA - Dubban muminai da mabiya tafarkin Ahlulbaiti (AS) ne suka shafe daren jiya suna addu’a da addu’o’i a hubbaren Imam Husaini (AS) a daren Lailatul Kadri na biyu, wanda ya yi daidai da zagayowar ranar shahadar shugaban masu tauhidi Ali (AS).
IQNA – Abin da ke tafe shi ne karatun kur’ani Tartil juzu’I na 21, wanda wasu fitattun qari na Iran suka gabatar: Jafar Fardi, Ali Kamran, Mojtaba Parvizi, da Mohammad Hassan Movahedi.
IQNA – Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa wajibi ne al'ummar Iran da sauran al'ummomin musulmi su koma Nahj al-Balagha domin daukar darasi daga Imam Ali (AS).
IQNA - An gudanar da Sallar Juma'a a mako na uku na watan Ramadan a Masallacin Al-Aqsa, duk kuwa da tsauraran takunkumin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta yi, tare da halartar Palasdinawa 80,000.
IQNA – Abin da ke tafe shi ne karatun kur'ani Tartil juzu'i na 20, wanda wasu fitattun qari na Iran su hudu: Hossein Rostami, Seyyed Mohammad Kermani, Vahid Barati, da Mohammad Javad Javari suka gabatar.
IQNA - Wani nazari da aka yi na wani littafi da ya koyar da yara masu amfani da harshen Faransanci kur’ani ya bayyana irin kalubalen da marubuta a wannan fanni ke fuskanta a cikin al’ummar da ba ruwansu da addini.
IQNA - Rundunar ‘yan sandan birnin Sydney ta sanar da cewa tana gudanar da bincike kan wadanda suka aikata wannan aika-aika bayan da suka samu wata barazana a kan masallacin Imam Ali (AS) da ke birnin Sydney.
IQNA – Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana sabbin hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kaiwa Gaza a matsayin babban laifi na gaske.