IQNA

Limamai A Kasar Canada Sun Yi Allawadai Da 'Yan ta'addan ISIS

20:53 - August 24, 2014
Lambar Labari: 1442674
Bangaren kasa da kasa, kwamitin limaman musulmi a kasar Canada ya yi kakkausar da yin Allawadai da ayyukan ta'addanci da kungiyar ISIS take aikatawa da sunan addinin musulunci a cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CCI cewa, a wani taro da ta gudanar, majalisar limaman musulmi a kasar Canada ta yi kakkausar da yin Allawadai da ayyukan ta'addanci da kungiyar ISIS take aikatawa da sunan addinin musulunci a cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya musamman a cikin kasashen Iraki da Syria a cikin lokutan nan.
Wasu rahotanni sun ce 'yan ta'addan ISIS sun tarwatsa wasu motoci biyu da suka shakare da bama-bamai a yau a garin Kazimiyyah na kasar Iraki, inda suka kashe fararen hula arba'in da takwas tare da jikkata wasu, wannan hari ya zo ne kasa da sa'oi ashirin da hudu da kai wani makamancinsa da 'yan ta'addan na ISIS suka yi a birnin Bagadaza, inda a nan ma suka kashe fararen hula fiye da hamsin tare da jikkata daruruwa.
Mayakan kungiyar ISIS da ke samun goyon bayan Amurka, Saudiyyah, Turkiya da kuma Isra'ila, sun kwace iko da wasu kauyukan kurdawa da ke kusa da garin Mausil, amma mayakan Kurdawa tare da taimakon jiragen yakin kasar Iraki sun samun nasarar fatattakar 'yan ta'addan na ISIS, duk kuwa da cewa dubban daruruwan mutane mazauna kauyukan sun kaurace ma yankunansu.
A bangare guda kuma 'yan ta'addan na ISIS sun sanar da cewa sun fara sayar da matan da suka kame kuma suke garkuwa da su a garin Mausil a matsayin bayi, yayin kwamandoji daga cikinsu suke zabar wadanda suka yi musu a matsayin kuyangi.
1442147

Abubuwan Da Ya Shafa: canada
captcha