IQNA

'Yan Ta'addan Najeriya Sun Sanar Kafa Daular Khalifancin Musulunci

22:35 - August 26, 2014
Lambar Labari: 1443522
Bangaren kasa da kasa, Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya ya ce yankunan da su ka kwace sun shiga karkashin ikon abin da ya kira “Daular Musulunci” day a ce sun kafa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran kasar Faransa cewa, a wani faifan Video wanda kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya sami kwafi, Abubakar Shekau ya ce; “Muna yi wa Allah godiya wanda ya bai wa ‘yan’uwanmu nasara a cikin wannan watan a garin Gwoza wanda ya shiga karkashin halifancin Musulunci.”

Bugu da kari  a cikin faifan video din mai tsawon minti 52 Abubakar Shekau ya  sake jaddada goyon bayansa ga Abubakar Bagadadi shugaban Daular Musulunci ta Iraki da Sham, wanda kuma shi ma ya nada kanshi halifan musulmi.

Babu tabbaci ko Abubakar Shekau din ya nada kanshi ne a matsayin halifa ko kuma ya yi wa Abubakar Bagadadi mubaya’a ne.

Wani daga cikin na hannun damar Shekau da ya bayyana a cikin faifan vedio din ya bayyana cewa; Za su ci gaba da zama a cikin garin na Gwoza ba za su  fice daga cikinsa ba.      

1443021

Abubuwan Da Ya Shafa: Shekau
captcha