Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misral Yaum cewa, hukumar kula da ayyukan addini a Masar ta samar da wani sabon tsari na koyar da karatun kur'ani mai tsarki da kuma hardarsa ta hanyoyi na zamani a kasar baki daya, wanda za a rik amfani da shia amakarantu.
Jami’an tsaro a kasar Masar sun sanar da samun kawunan mutane hudu da aka sare a yankin Sina a yau laraba. Majiyar tsaron ta ce mazauna garin Sheikh Zuwaid da ke yankin Sina ne su ka gano mutanen hudu da aka sarewa kawunan tare da zangin masu wuce gona da iri na addini da yin hakan. Majiyar ta ci gaba da cewa abu ne mai yiyuwa masu tsattsauran ra’ayin addinin sun kashe mutanan ne bisa zargin cewa suna aiki da jami’an tsaro domin basu bayanai.
Tun kwanaki biyu da su ka gabata ne dai aka sanar da bacewar mutanen a yankin na Sina. Sojojin Kasar Masar suna fada da kungiyoyi masu wuce gona da iri na addini da ke yankin na Sina saboda hannun da su ke da shi na kai hare-haren ta’addanci a cikin kasar Masar tun a cikin shekara ta dubu biyu da uku.