Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Akhbar Libya cewa, tun jiya ne aka fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki akasar Libya da ta hada bangarorin kasar domin kara karfafa makaranta da mahardata kan karatu da kuma hardarsu a fadin kasar ta Libya.
Wasu rahotanni daga birnin Tripoli na kasar Libya sun ce an yini ana barin wuta a cikin wasu unguwanni da ke birnin tsakanin wasu masu dauke da makamai, tare da jin karar fashewar wasu abubuwa.
Rahotannin sun ce barin wutar yana da alaka ne da yunkurin da gungun wasu 'yan bindiga suke yi ne kwace iko da wasu unguwanni a cikin birnin daga hannun wani gungun 'yan bindigar, lamarin da ya jawo fada mai tsanani a tsakaninsu, sabbin mahukuntan na Libya dai ba su komai kan lamarin ba.
Wasu bayanai sun ce wasu 'yan bindigar sun kai farmaki kan wani katafaren gini mallakin ofishin jakadan kasar Amurka a birnin Tripoli, inda suka mamaye ginin. Tun kafin wanann lokacin dai gwamnatocin kasashen turai da suka taimaka ma 'yan bindigar wajen kifar da gwamnatin marigayi Gaddafi, sun umarci jakadunsu da ma'yan kasarsu da su fice daga kasar ta Libya, sakamakon yadda tashe-tashen hankula suke ta kara tsanani a kasar.