IQNA

Kasashen Masar Da Maroco Za Su Yi Aikin Buga Kur’ani Tare

17:50 - September 14, 2014
Lambar Labari: 1450010
Bangaren kasa da kasa, kasashen Masar da Moroco za su gudanar da aiki tare domin buga kwafin kur’ani mai tsarki kamar dai yadda wakilan dukkanin bangarorin biyu suka cimma yarjejeniyar hakan a jiya a birnin Alkahira na kasar Masar.

 Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Manarah cewa, a jiya kasashen Masar da Moroco sun amince kan cewa za su gudanar da aiki tare domin buga kwafin kur’ani mai tsarki kamar dai yadda wakilansu suka cimma yarjejeniyar hakan tare da rattaba hannu, kuma za a gudanar da aikin ne a tsakanin shekarun 2014, 2015 da kuma 2016.
Ministan harkokin addini na kasar Masar Muhammad Mukhtar Juma’a tare da jakadan kasar Moroco ne suka cimma wannan yarjejeniya a jiya  abirnin na Alkahira fadar mulkin kasar Masar, inda suka jaddada wajabcin yin aiki tare a dukkanin bangarori na yada addinin muslunci tare da fito da hakikanin fuskarsa ta zaman lafiya da koyarwar kur’ani mai tsarki ga sauran al’ummomi.
Haka nan kuma bangarorin biyu sun amince kan cewa za su baya buga kur’ani mai tsarki, za su aiki a wasu fagagen na daban, da hakan ya hada da buga wasu littafan na addini da kuma yada al’adu na musulunci gami yada su zuwa kasashen kertare musamman ma  akasashen da ban a larabawa ba, domin su kara samun masaniya dangane da addinin muslunci da kuma al’adunnsa.
1449735

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha