
Kamfanin dillancin labaran ina ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-bilad cewa, babban jami'I a ma'aikatar kula da harkokin addinai ta kasar Algeriya Sayyid Da'as ya bayyana ana shirin gudanar da wani shirin jarabawa ga limamai da ladanai na kasar a karkashin ma'aikatar mai kula da harkokin addinin muslunci, wanda za a fara daga gobe.
Ya ci gaba da cewa kimanin limamai da ladanai 1150 ne za su shiga cikin wannan jarabawa bayan sun rijistar sunayensu, kimanin 500 daga cikinsu za a nada su ne a matsayin limamai yayuin da kimanin 250 kuma a matsayin malamai da za su rika koyar da karatu da sauran ilmomi na kur'ani mai tsarki a makarantu duk a karkashin ma'akatar.
Babbar manufar wannan shiri dai it ace samar da malamai da za su rika yin limamanci da ake da tabbaci dangane da masaniyarsu da addinin muslunci, domin kuwa dukkanin wadanda za a yi ma jarabawar dalibai ne da suka kammala karatunsu a jami'a a bangarori na ilmomin addinin muslunci, saboda haka babu shakku a kan karancin ilminsu, dukkaninsu malamai da suke da masaniya kan addini tare da iya yi ma mutane bayani kan addini da kuma koyar da su a makarantu da masallatai.