
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya naalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saida online cewa, a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar juma’a a jiya babban sakataren cibiyar malaman gwagwarmya Sheikh Mahir Hammud ya bayyana a masallainsa na Saida cewa yahudawan sahyuniya su ne yahudawan da aka yi ishara da su a cikin kur’ani mai tsarki tun tsawon karnoni da suka gabata.
Wasu yahudawa sahyuniya 'yan kaka gida masu tsatsauran ra'ayi dauke da bindigogi sun banka ma wani masallaci wuta a kauyen Al-mugir da ke yankin gabar yamma da kogin Jordan, inda suka kone shi kurmus.
Jami'an gwamnatin kwarya-kwarya cin gishin kai ta Palastinawa sun ce yahudawan sun killace masallacin ne suna dauke da makamai, ta yadda Palastinawan da ke wurin ba za su iya tunkararsu ba, inda suka banka wuta kan masallacin tare da cikakkiyar masaniya daga jami'an tsaron Isra'ila, wanda kuma ba shi ne karon farko da suke yin hakan ba a wannan kauye, inda a cikin 2012 sun kone wani masallaci a wurin.
A cikin 'yan kwanakin nan dai yahudawan sahyuniya suna kai farmaki kan yankunan palastinawa da ke gabacin birnin Qods da kuma gabar yamma da kogin Jordan, inda suke kone masallatai da kuma makarantu gami da kaddarorin palastinawa, kamar yadda jami'an tsaron yahudawan na Isra'ila suke bi gida-gida suna kame matasa.
1473264