IQNA

Haramtacciyar kasar Isra’ila ta rufe cibiyar koyar da Alkur’ani a kuduncin Masallacin Kudus

13:58 - February 07, 2009
Lambar Labari: 1741248
Bangaren hulda ta kasa da kasa: sojojin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila a safiyar ranar 16 ga watan Bahman ne suka kai wa cibiyar koyar da Alkur’ani da hardarsa ta Zaid bin Sabit a garin kudus mai girma kuma da yake kuduncin masallacin Kudus hari da rufe wannan cibiya.
Cibiyar koyar da Alkur’ani ta Iqna bayan nakalto daga majiyar Ma’a ta watsa labarin cewa: sojin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai mamaye da makamai kan cibiyar koyar da alkur’ani ta Zaid bin Sabit a garin Kudus tare da yin awangaba da duk wani abu da ke cibiyar.

Har ila yau sojin Isra’ila sun bude wuta kan mutanan yankin domin hana su kusantar cibiyar da hana yan gwagwarmaya isa gurin.Bugu da kari sojin gwamnatin Haramtacciyar kasar ta Isra’ila sun tsare Sufiyan Jadullah shugaban cibiyar ta Zaid bin Sabit tare da wulakanta takardun Alkur’ani a cibiyar.


359271
captcha