Cibiyar koyar da Alkur'ani ta Iran Iqna bayan ta nakalto daga gidan talbijin na" Rusiyal Yom" ta watsa rahoton cewa: Witali Corkin a wannan karo ya bayyana cewa: zaman taron kasa da kasa kan sake gina Gaza zai samu halartar manyan yan siyasa daga kasashe daban-daban na duniya kuma za a gudanar da shi ne bayan zaman sake gina Gaza a birnin Alkahira.
Ya kara da cewa:Diplaumasiyar Rasha za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da sauran kasashen duniya domin warware matsalolin da ke addabar duniya kuma zaman sake gina Gaza na daga cikin rawar da diplaumasiyar Rasha ke takawa na ganin an samara da sulhu da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da gaggauta gina Gaza.A bangare daya ya bukaci gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila da ta bude dukan mashigar Gaza domin isar da kayayyakin agaji da magunguna da kuma aiki da bukatar komitin tsaro na majalisar dunkin duniya da dokokin kasa da kasa da suka shafi kare hakkin fararen hula. Ya kuma jinjina muhimmancin tsagaita wuta da sulhu mai daurewa a yankin da damawa da dukan kasashen duniya da hukumomi na kasa da kasa wajen sake gina Gaza.
359439