Cibiyar kula da harkokin alkur'ani ta Iran Ikna ta nakalto daga kamfanin dillancin labaran Iraki cewa; ministan harkokin wajen kasar Faransa ya sanar a cikin wani bayani day a fitar jiya cewa; Faransa tana yin Allawadai da hare-haren ta'addanci kan masu ziyarar Imam Hussain a karbala.
A ci gaba da kai hare-hare ta'addanci kan masu ziyarar Karbala domin halartar tarukan cika kwanaki arba'in na shahadar Imam Hussain, mutane da daman e suka yi shahada, inda a ranar Asabar mutane 40 suka yi shahada wasu 80 kuma suka jikata bayan kai harin kunar bakin wake a kansu.
364470