Bangaren kasa da kasa: Tal'at Tajuddin, shugaban cibiyar kula ayyukan addinin musulunci a kasar Rasha, ya bayyana cewa za a bude babbar cibiyar addinin musulunci mafi girma Rasha a yankin Gurgan.
Kamfanin dillancin labaran ikna, ya nakalto daga jaridar Albasha'ir cewa; Tal'at Tajuddin ya bayyana cewa cibiyar da za a bude a yankin Gurgan, ita ce cibiya mafi girma ta koyar da addinin musulunci da za a bude a kasar Rasha, inda wasu daga cikin malaman addinin musulunci na kasar Rasha za su bayar da gudunmawa wajen koyar da addinin musulunci a cibiyar, kuma za a koyar da wasu yaruka da ka'idojinsu, daga cikin yarukan kuwa har da yaren larabci, da yaren Farisanci da kuma yaren kasar ta Rasha.
364533