Bangaren kasa da kasa: An bude gasar karatu da hardar alkur'ani mai tsarki ta mata a karo na biyar a birnin Tripoli na kasar Libya, inda taron ke samun halartar dalibai da malaman makarantu da ma jami'an gwamnati.
Cibiyar kula da harkokin alkur'ani ta Ikna, ta nakalto daga jaridar (Alfaj Jadid) cewa; an fara gudanar da gasar karatun alkur'ani a birnin Tripoli nakasar Libya, wanda kuma cibiyar kula da ayyukan alkairi ta kasar ce ta shirya gudanar da gasar a babban ginin cibiyar (Nur) da ke birnin Tripoli. Bayanin ya kara da cewa mata 61 ke halartar gasar, inda wasu daga ckinsu suna bangaren hardar dukkanin alkur'ani ne, wasu kuma bangaren rabin kur'ani, wato juzu'I 15, wasu daga cikinsu kuma bangaren kira'a.
365168