Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran SPA cewa; limamin masallacin Quds ya bayyana cewa yahudawan sahyuniya na da shirin rushe masallacin Quds, domin kuwa har yanzu suna ci gaba da gina manyan ramuka a karkashin masallacin, wanda hakan zai iya yin sanadiyar ruzawarsa a kowane lokaci. Ya ce wajibi da ya rataya kan al'ummar musulmi su dauki dukkanin matakan da suka dace domin takawa yahudawan sahyuniya birki, kan wannan mummunar aika-aika.
Limamin ya yi Allawadai da rushe gidajen Palstinawa 88 da Isra'ila ta yi, tare da fitar da palastinawa sama da 1500 daga yankunansu da ke gabacin birnin Quds.
368447