Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP cewa; daya daga cikin jagorin musulmin kasar Rasha Abdulbari Moslimov ya bayyana cewa, mafi yawan msulmin Rasha musamman a yankin Nijni Novgorod suna sayen furanni ne da ake zowa da su daga kasar Holand, amma sanadiyar shirya wani fim da aka yin a ci zarafin manzon Allah (SAW) a kasar, suna kiran dukkanin musulmi da su kaurace wa sayen furannin na Holand, domin kare matsayin manzon Allah tsirar Allah da amincinsa su tabbata gare shi da iyalan gidansa.
369932