IQNA

Coci a Damaskos Ta Yi Allah Wadai da Cin Mutuncin Addinin Kiristanci da HKI Ke yi

16:34 - February 28, 2009
Lambar Labari: 1749559
Bangaren kasa da kasa: Cocin Intakiya a birnin Damaskos babban birnin kasar Surya ta yi Allah wadan gidan Talbijin din HKI na goma da Ya watsa cin mutuncin Annabi Isa(AS) da Maryam (AS).
Cibiyar da ke kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labaraia ta Sana ta watsa rahoton cewa: abubuwan da gidan talbijin din HkI na goma ya watsa kan cin mutuncin Annabi Isa (AS) da kuma Ma'aifiyarsa Marya (AS) karya ce tsagwaramta a fili abin Allah wadai ne kuma wannan ya fito da hakikanin Yahudawan sahayoniya da irin yadda suka yi wa abubuwa masu kima da daraja na sauran addini .Kuma wannan ya fito da yadda a fili HKI da yahudawan Sahayoniya ke cin mutunci da taka dokokin kasa da kasa hatta da na addini da mutunta akidun sauran addinai.

369761

captcha