Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wata zantawa da ta hada shi da shugaban kwamitin kula da al'adu na jami'ar Mostafa (SAW) ya bayyana cewa; an fara gudanar da gasar share fagen ne bangarori daban-daban na kur'ani, da hakan ya hada da karatu kur'ani amma da kira'ar tartili, gami da hardarkur'ani a matakai daban-daban.
Ya kara da cewa; za a ci gaba da gudanar da gasar na tsawon 'yan kwanaki, inda da a bangare guda kuma na gasar za a yi tambayoyi kan wasu hadisai, da hakan ya hada hardar mataninsu da kuma kiyaye hakikanin ma'anoninsu.
Ya ce dalibai da daman e daga kasashen duniya da suke karatu karkashin jami'ar su shiga gasar.
372956