IQNA

An Karanta Bayanin Karshe Na Taron Makon Hadin Kai

12:36 - March 17, 2009
Lambar Labari: 1756713
Bangaren kasa da kasa: Mahalarta taron makon hadin kai a karo na ashirin da biyu a cikin bayanin karshen taro, sun yi Allahwadai da hare-haren baya-bayan nan da Haaramtacciyar Kasar Isra'ila ta kaddamar kan al'ummar Gaza.
Kmafanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; mahalarta taron makon hadin kai a karo na ashirin da biyu a cikin bayanin karshen taro, sun yi Allahwadai da hare-haren baya-bayan nan da Haaramtacciyar Kasar Isra'ila ta kaddamar kan al'ummar Gaza, tare da jaddada wajabcin tarbiyantar da masu tasowa kan koyrwa ta addini da gwagwarmaya domin daukakar addinin Musulunci. Mahalarta taron sun a cikin bayanin karshe sun bayyana cewa al'ummar musulmi na fuskantar babbar barazana daga waje, wanda hakan na bukatar namijin kokari daga al'ummar musulmi wajen fuskantar wannan barazana, wanda kuma ba za ta kasance ba sai al'umma ta hada kanta.

378377

captcha