Bangaren kasa da kasa: Mun ga yadda mutane Gaza suka yi nasara a yakin baya-bayan nan, mun ga yadda Hamas ta jagoranci yaki na addinin Musulunci a kan karya da zalunci, shahidanmu wadanda suka riga mu samun shahada ci gaba da tafarkin jihadi wata babbar amanarsu ce a kanmu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wani bayani da jakadan Palstinu a Iran (Salhuddin Zawawi) ya gabatar a wajen taron makon hadin kai da aka gudanar a birnin Tehran ya bayyana cewa; mun ga yadda mutanen Gaza suka yi nasara a yakin baya-bayan nan, mun ga yadda Hamas ta jagoranci yaki na addinin Musulunci a kan karya da zalunci, shahidanmu wadanda suka riga mu samun shahada ci gaba da tafarkin jihadi wata babbar amanarsu ce a kanmu, saboda haka ci gaba da bin tafarkin jihadi kiyaye amanrsu ne a kanmu.
A bangare guda kuma ya taya dukkanin al'ummar musulmi murnar zagayowar wadannan ranaku masu albarka, na tunawa da haihuwar fiyayyen halitta ma'iki (SAW) ya ce babbar manufarmu ita ce ci gaba da tafarkin manzon Allah ba tare da jin tsoron zargin mai zargi ba.
378467