Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Arab News) cewa; magajin garin Makka (Khalid Failsa) ya bayyana cewa; addinin Musulunci addini ne na ci gaba da bunkasa da adalci gami da 'yanci, ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban daliban jami'a da suka taru a jami'ar sarki Abdulaziz da ke birnin Jiddah, ya ce farfagandar da wasu ke yi kan addinin Musulunci da nufin bata surarsa a idon al'ummomin duniya, wannan mummunan aiki ne ya cancanci yin Allawadai da shi, domin kuwa a cewarsa addinin Musulunci addini ne da ya kawo wad an adam dukkanin ci gaban rayuwa a dukkanin fuskoki.
Wannan dai shi ne karo na farko da ya fara gabatar da irin wannan jawabi a gaban daliban jami'a a birnin Jiddah, kuma za a ci gaba da hakan a kowace shekara.
375946