Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; an buga tare da yada kur'ani mai ruwan zinari wanda Dokta Shauki ya rubuta a cikin shafuka 240, tare da kawata rubutun da kaloli masu ban sha'awa. Marubucin ya yi amfani da salon a musamman wajen rubuta wannan kur'ani, inda yakan ambaci sunayen wurare da wasu abubuwa suka faru da kur'ani ya mabata, tare da bayyana sunayensu na dad a kuma sunayensu na yanzu, tare da bayyana inda wuraren suke a halin yanzu a doron kasa, daga cikin irin wadannan wuraren kuwa akwai wurin da jirgin annabi Nuhu ya tsaya bayan kwaranyewar ruwan Dufana, da wurin Ahkaf, da kuma wuraren Ashabul kahf, da Madyana da dai sauransu. Kamar yadda ya ambaci wuraren halittun nan na yajuju wa majuju, da sa'ibun gami da banu kainuka'a da Khaibar, da dai sauran wurare da suka shafi tarihin manzon Allah da sahabbansa da kuma yakokin da aka yi a wancan lokaci.
379607