Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (straits Times) cewa; an kammala gyaran ginin tsohon masallacin nan na birnin Singapore, inda aka bude wata cibiyar ilimi a cikinsa domin koyar da ilmomin kur'ani mai tsarki, rahoton ya ce wannan babbar cibiya tana hade dad akin karatu, wanda aka cika shi da littafai na addini a fagage daban-daban, kamar yadda cibiyar take da azuzuwa na karatu domin koyar da ilmomin kr'ani, da hakan ya hada da kira'a, sanin ka'idojin karatun karatun kur'ani wato tajwidi, kamar yadda yanzu hakan an samara da gogaggun malamai da za su iya koyarwa a wannan cibiya, haka nan kuma tuni aka fara yin rijistan sunayen dalibai da za su yi karatu a wannan cibiya.
Shugaban cibiyar (Allamah Musa) ya bayyana cewa da yardarm Allah za su yi amfani da salo mafi dacewa wajen koyar da ilimin kur'ani mai tsarki.
380557