Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran interfax cewa; a wata ganawa da ta hada sakataren kungiyar kasashen musulmi da shugaban kasar Rasha a jiya a birnin Moscow, Shugaban kasar Rasha Dmitry Medvedev ya jaddada cewa gwamnatin kasarsa na son ganin ta kara karfafa dangantaka da kungiyar kasashen musulmi. Ya ci gaba da cewa kasar Rasha kasa ce mai addinai daban-daban, da suka hada da mabiya addinin Musulunci, a kan haka yana da matukar muhimmanci ta kara karfafa dangantaka tsakanin kungiyar kasashen musulmi, domin kuwa hakan na da matukar alfanu ga gwamnati da ma mabiya addinin Musulunci na kasar.
A nasa bangaren sakataren kungiyar kasashen musulmi ta OIC Ikmaluddini Ihsan Uglo ya bayyana cewa; ko shakka babu kasashen musulmi za su karbi Rasha hannu biyu-biyu a cikin kungiyar.
380744